Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Kudancin Nijeriya (Nollywood), Akindele, ta karɓi addinin Musulunci kuma ta sauya suna zuwa Khadijah, lamarin da ya sanya jama’a cikin mamaki da fatan alheri.
Hankula sun tashi a duniya musamman a arewacin Najeriya, bayan da labari ya karade kafafen sada zumunta cewa fitacciyar jarumar Nollywood, Akindele, ta karɓi addinin Musulunci tare da zabar suna Khadijah.
Wannan muhimmin mataki da ta dauka ya jawo cece-kuce da fatan alheri daga masoyanta da sauran jama’a.
Haka zalika, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kafafe daban-daban, inda wasu ke yi mata addu’ar samun nasara a sabon tafiyarta na rayuwa, yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin ci gaba mai kyau.
Ko shakka babu, sauyin addini da sunan da Akindele ta yi ya kara fito da ita a matsayin jaruma mai jarumata ka da kokari aka abunda tasa gaba.
Wannan lamari na sauyawa daga addini zuwa wani addini ba abu bane da ake yawan samu musamman a tsakanin manyan taurari a fagen wasan fina-finai na Nijeriya, hakan ya kafa tarihi a bangaren Nollywood.






