
Gwamnatin Najeriya ta ce duk wasu kudade da ake samu a kasar sun kai a biya musu haraji, ciki kuwa har na mata masu zaman kansu.
Jaridar Punch ta ruwaito shugaban kwamitin kudi da sauye-sauyen haraji na tarayya Taiwo Oyedele na bayyana haka a wani faifan bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo.
A cewar sa, duk wani kudi da za a biya don wani aiki wajibi ne a biya masa haraji, ko da kuwa ba ta hanyar halal bane.
Oyedele ya ce duka wannan na kunshe ne a dokar da ta kafa tsarin biyan haraji a Najeriya.
Leave a Reply