Wani lamari mai matuƙar tayar da hankali ya girgiza al’ummar Potiskum bayan wata sabuwar amarya ake zargin ta da aikata mummunan hari kan mijinta a daren farko na aurensu.
Ga cikakken rahoton yadda lamarin ya faru.
Amarya Ta Yanke Azzakarin Mijinta a Potiskum
Wani al’amari mai tayar da hankali ya faru a garin Potiskum, inda wata sabuwar amarya mai suna Khadija Jamilu, mai shekaru 18, ake zargin ta da yanke azzakarin mijinta mai shekaru 25.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da angon ya je wajen amaryarsa domin fara zamantakewar aure.
A cewar majiyoyi, ana zargin amaryar ta riga ta tanadi wuka, inda a yayin da mijin nata ke cire kaya, sai ta sare masa azzakari tare da tserewa daga wurin.
An ce angon ya samu mummunan rauni, amma an garzaya da shi asibiti cikin gaggawa domin ceton rayuwarsa.
Likitoci na kokarin ceto shi yayin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumomi sun bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin wannan lamari.






