Jaruma Asma’u Wakili ta bayyana nadamarta kan fitowa ba tare da dankwali ba. Ta ce daga yau za ta daina yin hakan, amma wando ba zai gagare ta ba, sai dai za ta kula da wane iri zata saka. Asma’u ta kuma yi kira da a daina saka bidiyon ƙananan yara suna rawa, tana mai cewa laifi ne kuma bai dace ba.
Jarumar Kannywood, Asma’u Wakili, ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta sake yin bidiyo ba tare da dankwali ba, saboda ta fahimci hakan kuskure ne.

Duk da haka, ta ce bata da damar daina sa wando gaba ɗaya, sai dai ta san irin salon da zai dace da ta dinga sakawa.
Asma’u ta bayyana hakan ne a yayin da take nuna rashin jin daɗinta game da wani bidiyo da ake yayatawa, na wata karamar yarinya ƙasa da shekara biyar tana rawa a gidan solo.
Ta yi kira ga masu wannan aiki da su ji tsoron Allah su daina, domin bai dace a rika saka yara ƙanana suna yin irin wannan rawa ba.
Kalla Bidiyon Asma’u Wakili Anan!






