A jihar Enugu, wani mai wa’azi, Evang. Ebube Joseph, ya jagoranci gagarumar zanga-zanga yana roƙon Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya taimaka wa Kiristoci a Najeriya da ke fuskantar tsatsauran rikici da tashin hankali a wasu ƙauyuka.
Evang. Ebube Joseph ya fito tare da tawagarsa a titunan Enugu suna ɗauke da faifai da sakonnin gaggawa, suna bayyana damuwa kan matsalolin tsaro da Kiristoci ke fuskanta, suna kuma rokon Amurka ta yi wani abu don kawo ƙarshen wannan hali.
Da yake zantawa da manema labarai, Evang. Joseph ya ce:
“President Trump, don Allah kada ka ba mu kunya. Har yanzu muna jira sojojin Amurka, kisa yana ci gaba da faruwa, mutanenmu na cikin tashin hankali.”
Zanga-zangar ta ja hankalin jama’a da masu bibiyar al’amura a yankin, inda da dama suka bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro da yadda mutanen ke fara neman mafita daga ƙasashen waje.
Evang. Joseph ya nemi shugabannin kasashen duniya su duba wannan al’amari da idanun rahama, tare da samar da taimakon jin kai da na tsaro ga al’ummomin da ke cikin hatsari.






