“Nakan riƙa tafiya kafaɗata a ɗage saboda girman nonuwana, kuma kunya kan kama ni a duk lokacin da na haɗu da mutane,” in ji wata mata da ta daɗe tana fama da matsalar manyan nonuwa.
A shekarar 2010, wata farfesa a ƙasar Argentina ta yanke shawarar yin tiyata domin rage girman nononta.
Yanzu tana da shekara 52, kuma ta ce aikin da aka yi mata ya ba ta wani sabon ƴanci da walwala da ba ta taɓa samu ba a baya.
Ko da yake manyan nonuwa na jan hankalin wasu maza a sassa daban-daban na duniya, a wani ɓangaren kuma suna iya shafar lafiyar mata da ingancin rayuwarsu.
Masana sun bayyana cewa manyan nonuwa na iya haddasa matsaloli da dama, ciki har da ciwon baya, ciwon wuya, karkatar jiki, rashin jin daɗin jiki, matsalar bacci, har ma da damuwar ƙwaƙwalwa.
Sabbin alkaluma daga ƙungiyar likitocin kwaskwarimar jiki sun nuna cewa an yi wa mata kusan 652,676 aikin rage girman nono a shekarar 2024.
Brazil ce ke kan gaba da yawan waɗannan ayyuka, inda aka yi kimanin 115,647.
Amurka ta biyo baya da 67,478, sai Faransa da 38,780, Jamus da 32,068, Turkiyya da 25,334, sannan Indiya da 22,400.
Raquel, wata mata da ta fuskanci irin wannan ƙalubale, ta bayyana cewa nonuwanta sun ƙara girma bayan ta shayar da ’ya’yanta biyu na farko.
Ta ce tun tana budurwa take fama da ciwon baya sakamakon girman nonuwanta, lamarin da ya shafi rayuwarta ta yau da kullum.






