Fitar maniyyi mai ƙarfi yana da muhimmanci ga lafiyar jima’i da haihuwa.
Rashin fitar maniyyi da ƙarfi na iya haifar da jinkirin samun ciki ko matsalolin haihuwa.
Ga wasu manyan dalilai guda 10:
—
1. Raunin Jijiyoyin Azzakari da Maraina
Yawan istimna’i a baya, sanyi, ko gajiya na rage ƙarfi da motsi na jijiyoyi masu taimakawa fitar maniyyi.
2. Raguwar Sinadarin Testosterone
Testosterone hormone ne mai muhimmanci wajen ƙarfafa fitar maniyyi da sha’awa. Raguwar sa na iya haifar da fitar maniyyi mai rauni.
3. Cunkoson Maniyyi a Hanyarsa (Blocked Ducts)
Idan hanyoyin da maniyyi ke bi sun toshe, fitarwa na iya zama mara ƙarfi ko jinkiri.
4. Cutar Prostate (Kumburin Prostate)
Prostate tana taka muhimmiyar rawa wajen tura maniyyi. Matsaloli a wannan sassa na iya rage ƙarfi da yawan fitar maniyyi.
5. Yawan Jima’i Ba Tare da Hutawa Ba
Jima’i mai yawa ba tare da hutu ba na gajiyar da jiki da rage ƙarfi na fitar maniyyi.
6. Ciwon Sanyi (STIs ko Cold Exposure)
Sanyi ko cututtukan jima’i na iya lalata jijiyoyi da ƙwayoyin maniyyi, suna rage ƙarfin fitarwa.
7. Ciwon Sukari (Diabetes)
Diabetes yana lalata jijiyoyi, ciki har da waɗanda ke taimakawa fitar maniyyi, wanda ke kawo matsala ga ƙarfin fitarwa.
8. Damuwa da Tunanin Stress
Tashin hankali ko damuwa na rage aikin kwakwalwa da jijiyoyin jima’i, wanda ke kawo raunin fitar maniyyi.
9. Rashin Bitamin da Ma’adanai
Vitamin da ma’adanai kamar Zinc, Vitamin E, da B-complex suna taimakawa ƙarfi da yawan maniyyi.
Rashin su na rage ƙarfin fitarwa.
10. Shan Magunguna ko Kayan Maye
Musamman taba sigari, giya, da wasu magunguna na rage ƙarfi da yawan fitar maniyyi.
—
Shawara
Idan kana fuskantar matsalar raunin fitar maniyyi ko bukatar ƙarin ruwan maniyyi, nemi shawara daga likita kafin ka yi amfani da magunguna ko karin sinadaran gaggawa.






