
Fitaccen mawaki Sadiq Saleh ya saki sabuwar wakarsa mai taken “Malamin Mata” a shekarar 2025. Wannan waka ta zo da sabon salo mai daɗi, musamman ga masoya wakokin Hausa da ke jin daɗin wakar soyayya.
“Malamin Mata” waka ce da ta nuna yadda daɗin soyayya ke juya rayuwa, har mutum ya manta da damuwa saboda ƙaunar da yake ji.
Sadiq Saleh ya haɗa kalmomi masu cike da ma’ana da kuma bajimta, wanda ke jawo hankalin masu sauraro.
Wakar ta samu karɓuwa a tsakanin matasa, musamman a kafafen sada zumunta, inda ake ta raba bidiyonta da sharhi mai gamsarwa daga masoya.





