Muhimmin abu da kowace mace ya kamata ta sani shi ne: ba duk lokacin da aka yi jima’i ake samun ciki ba.
Samun ciki yana faruwa ne kawai a wani takamaiman lokaci a cikin zagayowar jinin haila (menstrual cycle), lokacin da jikin mace ke sakin ƙwai (ovulation).
Idan aka yi jima’i a wannan lokaci, to damar samun ciki tana ƙaruwa sosai.
Menene Ovulation?
Ovulation shi ne lokacin da jikin mace ke sakin ƙwai daga mahaifa.
Wannan ƙwai ne idan ya haɗu da maniyyi (sperm) zai iya haifar da ciki.
Wannan shi ne lokaci kaɗai da mace ke da damar samun ciki cikin sauƙi.
Yadda Za Ki Gane Lokacin Ovulation
Domin gane wannan lokaci, mace na buƙatar ta san tsawon zagayowar jinin hailarta.
Misali:
Idan zagayowar jinin hailarki kwanaki 28 ne
Ki cire kwanaki 14 daga 28
Ranar da ta rage ita ce ranar ovulation
Ga mata da dama, ovulation na faruwa ne kusan kwanaki 14 kafin jinin haila na gaba.
Wane Lokaci Ya Fi Dacewa A Yi Jima’i?
Maniyyi (sperm) na iya rayuwa a cikin farji har kwanaki 5.
Saboda haka, ana ba da shawarar:
A yi jima’i kwanaki 5 kafin ranar ovulation
A yi jima’i ranar ovulation
A yi jima’i rana ɗaya bayan ovulation
Da wannan tsari, damar samun ciki na iya kaiwa kusan kashi 70%, idan babu wata matsalar lafiya.
Wasu Abubuwan Da Zasu Iya Hana Samun Ciki
Ko da an yi jima’i a lokacin da ya dace, wasu matsalolin lafiya na iya hana samun ciki, kamar:
Fibroid (ƙumburin mahaifa)
Toshewar bututun mahaifa (fallopian tubes)
Ovarian cyst
Cututtuka ko ƙwayoyin cuta a jiki
Saboda haka, lokaci kaɗai ba shi ne komai ba.
Muhimmin Shawara
Duk da cewa sanin lokacin ovulation yana da matuƙar muhimmanci, yana da kyau ma’aurata su je asibiti domin duba lafiyarsu.
Gwaje-gwaje na taimakawa wajen gano abin da ke faruwa a jiki da wuri.
Samun ciki yana buƙatar ilimi, lokaci mai dacewa, da lafiyar jiki.
Idan mace ta fahimci zagayowar jikinta kuma ma’aurata suka kula da lafiyarsu, damar samun ciki na ƙaruwa sosai.
Ina fatan kin amfana da wannan bayani.






