Fitaccen mawaki, Soja Boy, ya zo da sabuwar waka mai dauke da jigon soyayya mai suna “Habibi.” A wannan karon, ya hada kai da shahararriyar jarumar TikTok, Surayyah, inda suka nuna sha’awa da fasaha a cikin bidiyon waka.
Wakar “Habibi” ta Soja Boy tare da Surayyah ta kawo sabon salo da zazzafar saƙon soyayya cikin wakokin Hausa. Mawakin ya cike waka da kalmomin sha’awa, kauna, da jan hankali; yayin da Surayyah ta kara wa bidiyon waka armashi da kwarjini irin na jaruman zamani.
Wakar na daukar hankalin matasa a kafafen sada zumunta, musamman TikTok da YouTube. Yanzu haka, “Habibi” na samun karbuwa sosai a tsakanin masoya waka da masu sha’awar sabbin salon nishaɗi.






