Matsalar raunin ƙarfin jima’i na ɗaya daga cikin abubuwan da ke damun maza da yawa a wannan zamani.
Wasu mazan na fuskantar wannan matsala tun suna ƙuruciya, yayin da wasu kuma ke fara fuskanta bayan aure ko bayan shekaru.
Wannan na iya zama sanadiyyar damuwa, yawan tunani, rashin bacci, rashin motsa jiki, shan taba, giya, ko wasu cututtuka kamar hawan jini da ciwon suga.
A saboda haka, maza da dama kan nemi mafita ta hanyar magungunan bature da ake samu a chemist, domin ƙara ƙarfi, tsawaita lokacin saduwa, da samun gamsuwa a rayuwar aure.
Me Ake Nufi Da “Ƙarfin Maza” A Jima’i?
Ƙarfin namiji ba wai tsawon lokaci kawai ba ne, ya haɗa da:
Tsayuwar azzakari mai ƙarfi
Samun sha’awa (libido)
Jurewa ba tare da gajiya da wuri ba
Samun cikakkiyar gamsuwa bayan saduwa
Idan ɗaya daga cikin waɗannan na da matsala, to namiji na iya neman magani.
- Multivitamins Na Musamman Ga Maza
Waɗannan su ne kwayoyin vitamin da aka haɗa musamman domin lafiyar maza.
Abubuwan da suke ɗauke da su:
Zinc
Vitamin B6, B12
Vitamin D
Iron (a kaɗan)
Magnesium
Amfaninsu:
Ƙara kuzari a jiki
Rage gajiya da kasala
Inganta samar da testosterone
Taimakawa lafiyar maniyyi
Yadda ake amfani:
Ana shan kwaya 1 a rana bayan cin abinci.
Lura: Ba sa aiki nan take, suna aiki ne a hankali idan aka dage. - Zinc Supplement
Zinc muhimmin sinadari ne sosai ga lafiyar namiji.
Amfaninsa ga jima’i:
Ƙara yawan maniyyi
Inganta ingancin maniyyi
Ƙara sha’awa
Taimakawa tsayuwar azzakari
Gargadi:
Yawan shan zinc fiye da kima na iya haifar da:
Ciwon ciki
Tashin zuciya
Rage ƙarfin garkuwar jiki - L-Arginine
L-Arginine sinadari ne da ke taimaka wa jijiyoyin jini su buɗe.
Yadda yake aiki:
Yana ƙara yawo da jini zuwa azzakari
Yana taimakawa tsayuwar azzakari ta zama mai ƙarfi
Yana rage matsalar erectile dysfunction
Wanda bai kamata ya sha ba:
Masu hawan jini mai tsanani
Masu ciwon zuciya
Masu shan magungunan zuciya - Ginseng (Panax Ginseng)
Ginseng na daga cikin shahararrun magungunan bature a duniya.
Amfaninsa:
Ƙara sha’awar jima’i
Ƙara kuzari da nishaɗi
Rage damuwa da gajiya
Inganta aikin jijiyoyi
Ana samun sa a:
Kwaya
Syrup
Tea - Sildenafil (Viagra – ƙananan kashi)
Wannan magani na taimaka wa maza da ke fama da:
Rashin tsayuwar azzakari
Tsayuwar da ke gushewa da wuri
Yadda yake aiki:
Yana ƙara jini zuwa azzakari ne lokacin da aka samu sha’awa.
Muhimman gargadi:
Kada a sha tare da barasa
Kada a sha kullum
Kada masu ciwon zuciya su sha ba tare da shawarar likita ba - Magungunan Bature Na Ganye (Herbal Supplements)
Waɗannan ba na gargajiya kai tsaye ba ne, ana sarrafa su a masana’anta.
Abubuwan da suke ɗauke da su:
Maca Root
Tongkat Ali
Tribulus Terrestris
Amfaninsu:
Ƙara sha’awa a hankali
Ƙara ƙarfin jima’i ba tare da gaggawa ba
Inganta lafiyar maniyyi
Ka tabbata maganin yana da rajista kuma ba na jabu ba.
Abubuwan Da Zasu Ƙara Tasirin Magunguna
Ko da kana shan magani, idan baka kula da rayuwarka ba, sakamako zai yi ƙasa.






