Rashin ƙarfin mazakuta wata matsala ce da mazaje da dama ke fuskanta a ɓoye, duk da cewa tana da tasiri sosai ga rayuwar aure, lafiyar tunani, da zaman lafiya tsakanin ma’aurata.
A wasu lokuta, wannan matsala kan jawo sabani, damuwa, da rashin fahimtar juna a cikin aure.
Babbar matsalar ba wai rashin ƙarfin gaban kansa ba ce, illa hanyar da ake kallon matsalar da kuma yadda ake tunkararta, domin hakan ne ke ƙara tsananta al’amari. Saboda haka, fahimtar musabbabi, hanyoyin magancewa, da matakan kariya na da matuƙar muhimmanci.
Yaya Aikin Mikewar Gaba Yake A Jikin Namiji?
Mikewar gaban namiji yana faruwa ne ta haɗin gwiwa tsakanin manyan tsarukan jiki guda uku, wato:
Tsarin jijiyoyin sadarwa
Tsarin tsoka
Tsarin gudanuwar jini
Da zarar mutum ya ga ko ya yi tunanin wani abu mai motsa sha’awa, kwakwalwa na aika sako zuwa jijiyoyin da ke da alhakin mikewar gaba. Wannan sakon yana sa a saki wani sinadari mai suna Nitric Oxide, wanda ke ba da damar jini mai yawa ya rika shiga jijiyoyin gaban namiji, daga nan ne mikewa ke faruwa.
Tsawon lokacin da gaban namiji zai ci gaba da kasancewa a mike yana dogara ne da yadda waɗannan tsarukan ke aiki tare. Duk wata matsala da ta shafi ɗaya daga cikinsu na iya haddasa rashin ƙarfin mazakuta.
Me Ke Haddasa Rashin Ƙarfin Mazakuta?
Ba dalili guda ɗaya ke jawo wannan matsala ba. Sau da yawa dalilai da dama ne ke aiki tare. Ga wasu daga cikinsu:
Damuwa da fargaba
Rashin jituwa tsakanin ma’aurata
Matsalolin kwakwalwa kamar damuwa da tsananin tunani
Ciwon sukari da hawan jini
Illar wasu magunguna
Matsalolin jijiyoyin jini
Yawan cholesterol a jiki
Karancin sinadarin testosterone
Shan giya da taba
Tarin kiba
Rashin motsa jiki
Yawan cin abinci mai yawan sukari da mai
Yadda Ake Magance Rashin Ƙarfin Mazakuta Ta Hanyar Dabi’a
Maganin wannan matsala yana farawa ne da tantance musabbabinta. Saboda haka, magani na bukatar a duba bangarori fiye da ɗaya, kamar:
Lafiyar tunani
Salon rayuwa
Abinci
Shawarar likita
Shawarwari Masu Muhimmanci
Canza salon rayuwa ta hanyar barin shan taba da giya
Samun isasshen barci
Rage kiba ta hanya mai lafiya
Bin umarnin likita kan amfani da magunguna
Neman shawarar masana harkar kwakwalwa idan akwai damuwa
Cin abinci mai gina jiki da ke ƙarfafa jini da jijiyoyi
Mazaje da dama na neman magani ba tare da amfani da ƙwayoyi ba, kuma hakan yana yiwuwa idan aka bi hanya mai tsari da haƙuri.
Akwai wasu abinci na musamman da bincike ya nuna suna taimakawa wajen ƙarfafa mazakuta, amma za a tattauna hakan a rubutu na gaba, In shaa Allah.
Kammalawa
Rashin ƙarfin mazakuta ba kunya ba ne, kuma ba ƙarshen rayuwa ba ne. Matsala ce da za a iya magancewa idan aka nemi ilimi, shawara, da magani a kan lokaci.
Allah Ya bai wa duk masu fama da wannan matsala lafiya, Ya kuma sanya alheri da zaman lafiya a rayuwar aure.






