Innalillahi…
Ina gabatar da wannan rahoto ne domin neman shawara daga masu karatu, malamai, da masu ƙwarewa a harkar aure.
Wata budurwa ce da ta tuntube ni, tana cikin shirin aure da saurayin da suka daɗe suna soyayya.
Ta bayyana cewa a farkon al’amura suna tafiya cikin fahimta da mutunta juna. Amma daga baya, saurayin ya fara matsa mata da buƙatar abubuwan da ba ta yarda da su ba kafin aure.
A cewarta, ta sha nuna masa rashin amincewa, tana masa bayanin cewa tarbiyyarta da addininta ba su yarda da hakan ba.
Sai dai saurayin ya ci gaba da kawo hujjoji, yana cewa ai ba laifi ba ne, tunda sun kusa aure, kuma wai hakan zai hana matsala a nan gaba.
Matsin lambar ya ƙaru matuƙa har abin ya ketare iyakar da ta saka wa kanta. Wannan abu ya jefa ta cikin tashin hankali, nadama, da ruɗani. Tun daga wannan lokaci, ta fara tambayar kanta ko wannan soyayyar za ta kai ga aure mai albarka, ko kuwa alama ce ta matsala mai zuwa.
A yanzu haka, budurwar tana tsaka da shawara mai wuya:
Ta rabu da saurayin domin kare mutuncinta da imaninta,
ko
Ta ci gaba da soyayyar, tana fatan halin zai gyaru kafin aure.
Saboda haka nake gabatar da wannan rahoto a gare ku, masu karatu:
👉 Shin me ya dace ta yi a irin wannan hali?
👉 Shin matsin lamba kafin aure alama ce ta soyayya, ko rashin girmamawa?
👉 Idan kai ne ko ke ce a matsayinta, wane mataki za ka ɗauka?
Muna jiran shawarwarinku domin wannan rahoto ya zama darasi ga masu shirin aure.






