Bincike ya nuna cewa kusan kashi 70% na ma’aurata sun fi jin sha’awar jima’i a tsakar dare.
Wannan ya sa wasu ke ɗaukar yin jima’i da daddare a matsayin abu na yau da kullum.
Amma tambayar ita ce:
shin ya dace a tashi abokin zama daga bacci don neman jima’i?
Menene “Wake-Up Sex”?
A turance ana kiransa wake-up sex—wato a taso abokin zama daga bacci da nufin jima’i.
Wasu ma’aurata suna jin daɗin hakan, wasu kuma ba sa jin daɗinsa kwata-kwata.
Dalilan Da Ya Sa Zai Iya Rage Armashi
Masana sun nuna cewa yin jima’i ba tare da shiri ba na iya rage gamsuwa, saboda dalilai kamar haka:
Rashin shiri na jiki da tunani
Jima’i na buƙatar shiri a zuciya da jiki. Taso mutum daga bacci na iya barin jikinsa bai shirya ba.
Rashin warwarewar jiki
Wanda aka taso daga bacci na iya kasa gamsar da ɗayan saboda jiki bai warware ba.
Warinh baki da rashin sumbata
Ba kowa ne ke farkawa da baki mai daɗi ba. Rashin sumbata na iya rage kusanci da armashi.
Sauyin yanayin jikin mace yayin bacci
Wasu mata ba sa iya farkawa cikin sauri su shirya jiki don jima’i bayan dogon bacci.
Zuwan kai da wuri ga namiji
Idan mace ta taso miji daga bacci, akwai yiwuwar zuwan kai da wuri, wanda kan hana mace gamsuwa.
Mace na buƙatar lokaci don “ɗaukar zafi”
Mace tana buƙatar foreplay da lokaci kafin ta kai ga gamsuwa; taso ta daga bacci na iya hana hakan.
To, Me Ya Kamata Ma’aurata Su Yi?
Wannan ba yana nufin ba a yarda a tashi juna daga bacci ba ne. Abin da ya fi muhimmanci shi ne:
Sanin ra’ayin juna: Tabbatar abokin zama na jin daɗin irin wannan salo.
Ba wa jiki lokaci: A fara da hira, sumbata, da wasannin motsa sha’awa.
Guje wa gaggawa: Kada a tashi daga bacci a wuce kai tsaye zuwa jima’i.
Girmama yarda: Idan ɗaya bai shirya ba, a girmama hakan.
Abunda Yakamata Ku Sani:
Jima’i hanya ce ta kusanci da gamsuwa ga ma’aurata, amma shiri, yarda, da fahimtar juna su ne ginshiƙai.
“Wake-up sex” na iya zama daɗi ga wasu, amma ga wasu kuma yana rage armashi.
Abin da ya dace shi ne a yi abin da ya fi gamsar da ku duka biyun.
Gargadi: Wannan labari na ma’aurata ne kawai.






