Rashin ƙarfin mazakuta a lokacin saduwa (erectile dysfunction) matsala ce da maza da yawa ke fuskanta, amma galibi suna jin kunyar faɗa.
Wannan matsala tana iya shafar aure, kwanciyar hankali, da lafiyar tunani.
Abu mai kyau shi ne, a mafi yawan lokuta ana iya magance ta idan an fahimci dalilai.
- Damuwa da tunani
Yawan tunani, tsoro, ko damuwa game da aiki, kudi, aure, ko tsoron “zan iya gamsar da ita?” na rage iskar jini zuwa azzakari, hakan yana sa ya kasa tashi da kyau. - Gajiya da rashin bacci
Rashin hutu da gajiya suna rage hormones na maza (testosterone). Idan jiki ya gaji, sha’awa da ƙarfi sukan ragu. - Matsalolin jini da hawan jini
Azakkari yana bukatar isasshen jini domin tashi. Ciwon suga, hawan jini, ko toshewar jijiyoyi na iya hana jini gudana yadda ya kamata. - Yawan kallon batsa
Yawan kallon batsa na iya sa kwakwalwa ta saba da abubuwa masu tayar da sha’awa ta bogi, ta daina amsawa ga mace ta gaskiya. Hakan yana jawo rashin tashi ko gajeren lokaci. - Shan taba, giya, ko miyagun ƙwayoyi
Wadannan abubuwa na lalata jijiyoyin jini da hormones, suna rage ƙarfin azzakari da sha’awa. - Rashin motsa jiki da kiba
Kiba da zaman zama suna rage gudan jini da hormones. Motsa jiki yana taimakawa azzakari ya samu isasshen jini. - Matsalar aure ko rashin fahimta
Rikici, fushi, ko rashin jituwa da mata na kashe sha’awa, duk da jiki yana lafiya. - Wasu magunguna
Wasu magungunan hawan jini, damuwa, ko rashin bacci na iya rage ƙarfin mazakuta a matsayin illa.
Yadda za a kare kai
Yin motsa jiki akai-akai
Cin abinci mai lafiya
Barin taba da giya
Rage kallo da tunanin batsa
Samun isasshen bacci
Tattaunawa da mata da neman shawarar likita idan matsalar ta dade
Rashin ƙarfin mazakuta ba alamar rauni ba ne, matsala ce ta lafiya da tunani. Idan namiji ya kula da jikinsa da zuciyarsa, a mafi yawan lokuta ƙarfi da sha’awa suna dawowa.






