Musamman ga matan aure, ko mazajen su na da hali ko ba su dashi, za su iya dogara da wadannan sana’o’in daga gida.
- Catering / Abinci da Snacks
Me yasa? Abinci kullum ana buƙata: bukukuwa, taron aure, suna, ma’aikata.
Halal ne? Halal ne idan ana amfani da kayan halal, babu haramun (kamar giya ko naman alade).
Fa’ida: Mace za ta iya karbar oda daga gida, ta samu kuɗi ba tare da ta fita waje ba. - Tailoring & Fashion Design
Me yasa? Kowane gida na buƙatar kaya: school uniforms, hijabi, abaya, kayan yara.
Halal ne? Halal ne matuƙar ba a dinka kaya marasa kamun kai ko na assha ba.
Fa’ida: Sana’a ce da za ta iya girma daga gida har ta zama babban boutique. - Makeup & Gele Tying
Me yasa? Mata suna son kyau musamman a biki ko taro.
Halal ne? Halal ne idan ba a canza halittar Allah da haramun ba (misali tattoo ko gashin haram). Za a iya mai da hankali ga halal makeup (natural look).
Fa’ida: Ana iya yi daga gida, kuma koyarwa (training courses) na kawo kuɗi sosai. - Cosmetics / Turare / Skincare Products
Me yasa? Turare da tsafta suna da muhimmanci a Musulunci, Annabi (SAW) ya karfafa mu.
Halal ne? Halal ne idan kayan sun halal, ba su hada da najasa ko kayan giya ba.
Fa’ida: Perfume oil, incense, organic creams suna da kasuwa sosai musamman a WhatsApp da Instagram. - Hairdressing
Me yasa? Gyaran gashi da tsafta yana da muhimmanci gare mace a gida da wajen taro.
Halal ne? Halal ne idan ba a amfani da gashin mutum (human hair), kitso ko synthetic wigs da gyaran gashi na halal.
Fa’ida: Sana’a ce da za a iya shekaru ana yi a gida kuma tana kawo kuɗi. - Digital Skills (Graphics, Social Media Management, Content Creation)
Me yasa? Fasaha yanzu na ba da damar neman kuɗi daga gida.
Halal ne? Halal ne muddin ba a amfani da fasaha wajen yada alfasha, yaudara ko karya.
Fa’ida: Za a iya yin freelance daga gida, kasuwa har da na ketare ce. - Poultry / Animal Rearing
Me yasa? Kwai, kaza, raguna ko zuma kullum ana amfani da su a gida da kasuwa.
Halal ne? Halal ne saboda abinci ne, amma a kiyaye tsafta da dokokin shari’a.
Fa’ida: Za ta iya fara da kaji kaɗan, daga nan kasuwanci ya girma. - Bead Making / Jewelry
Me yasa? Beads da kayan kwalliya suna da kasuwa musamman a bukukuwa da suna.
Halal ne? Halal ne muddin kayan ba na haramun ba (misali zinari ga maza, ko kayan haram).
Fa’ida: Zai iya zama sana’ar gefe

Leave a Reply