Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan wani zazzafan gardama da ta tashi tsakaninsa da wani jami’in soja, LT A.M Yerima, kan batun wani fili da aka kwace a Abuja.
A ranar Talata, lamarin ya dauki hankalin jama’a yayin da Wike ke kokarin shiga wani filin da ake ta musayar zargi a kan sa tsawon lokaci, sai jami’in sojan ya hana shi shiga. Wannan ya haifar da hayaniya da zafin maganganu, inda Wike ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Yayin hira da manema labarai, Wike ya nuna cewa matsayin sa na Minista ba zai ba shi damar lamunci cin zarafi ko tsoratarwa ba, “Ni cikakken jarumi ne, babu wanda ya isa ya tsoratani ko yaci zarafina.” Ya jaddada cewa gwamnatin babban birnin tarayya Abuja tana gudanar da bincike kan matsalolin da ke tashi a yankin, tare da kokarin tabbatar da adalci da tsarin doka.
Wike ya soki jami’in sojan da laifin amfani da matsayinsa wajen kokarin tsoratar da ma’aikata, yana mai cewa, “I am an Officer. I am a commissioned officer. I have integrity. I won’t shut up. You cannot shut me up. We won’t kill anybody. I am not a fool. I am a 3 star general.”
A cewar Wike, ya kamata tsarin mulki da doka su zama ginshikin aiki a babban birnin tarayya, tare da girmama juna da kaucewa duk wani cin zarafi ko tsoratarwa da ka iya haifar da matsala. Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake jiran sakamakon shari’a daga hukumomin da suka dace.

Leave a Reply