
A wata hira da jaridar Arewa Jazeera ta yi da wata mata, ta bayyana yadda rayuwarta ta canza bayan mijinta ya kara aure.
Ta fara da cewa:
“Bayan mijina ya auri budurwa, ya tuntube ni inyi yi hakuri zai shafe kwanaki bakwai tare da ita kafin ya dawo dakina kamar yadda aka saba. Amma sai ya dauki sati biyu ba tare da ya dawo ba, daga bisani lokacin ya zo ya roke ni in kara masa sati biyu tare da sabuwa. Duk da raina ya baci, sai na daure na amince.”
“Da suka cika sati hudu tare, na fara period a ranar zan karbi girki. Mijina ya kuma roke ni in bari ya kwana da sabuwar amaryarsa saboda halin da nake ciki, na amince. Bayan kwana biyar da zan samu lafiya, sai hutun aikin mijina ya kare, zai koma Abuja. Ya zo ya ajiye takardu a gabansa yana son mu zabi. Ni na zabi ‘zaman gida’, ita kuma sabuwar amarya ta zabi ‘tafiya Abuja’. Mijina ya yi dariya, muka yi sallama.”
Ta ci gaba:
“Bayan yaje Abuja ya dawo hutun sati biyu kamar yadda ya saba sai ya barta a can, na lura da saƙonni na soyayya daga sabuwar amarya a wayar mijina; tana roƙonsa kada ya dade ba tare da ya koma can ba. Wannan abu ya dagula min rai, amma na daure. Bayan wani lokaci mijina ya shigo cikin gaggawa, wai an masa kira daga aiki. Na masa fatan alkhairi. Kafin ya fita falo, na fadi na suma – aka kai ni asibiti, har kwana daya muka dawo gida.”
“Tun daga wannan lokaci sabuwar amarya tana zuwa da kiransa tana jin halin da nake ciki. Har abokinsa ya kawo ta gidanmu, ta kwana biyu. Yanzu kuma, mijina zai koma Abuja, na shaida masa ko ta zauna sai ya hada mu duka mu tafi, domin na gaji da halin rashin tabbas.”
Ta kammala hirarta da kalmomin hakuri da tausayi, tana fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Leave a Reply