Rikicewar al’ada na nufin lokacin da haila ba ta zuwa a tsari: wani lokaci tana jinkiri, wani lokaci tana zuwa da wuri, ko kuma tana zuwa da yawa ko kaɗan.
Wannan matsala tana shafar mata da yawa, kuma tana iya samo asali daga hormone, damuwa, ko wata matsala a jiki.
Manyan Dalilan Rikicewar Al’ada
Rikicewar Hormone
Idan hormones kamar estrogen da progesterone sun rikice, haila ba za ta zo a daidai lokaci ba.
Damuwa da tashin hankali
Yawan tunani, damuwa, ko rashin barci na iya rikita aikin hormones.
Canjin nauyi
Yin kiba sosai ko yin siriri fiye da kima na iya shafar al’ada.
Polycystic Ovary Syndrome (PCOS)
Wata cuta ce da ke shafar ovaries, tana haddasa rashin al’ada da wahalar daukar ciki.
Magunguna
Wasu kwayoyi, musamman na hana daukar ciki, na iya rikita haila.
Hanyoyin Gyara Rikicewar Al’ada
- Gyara salon rayuwa
Cin abinci mai gina jiki
Shan ruwa da yawa
Motsa jiki akai-akai
Samun isasshen barci - Rage damuwa
Yin addu’a, yin atisaye, da hutawa suna taimakawa wajen daidaita hormones. - Shan wasu ganye na gargajiya
Wasu mata suna samun sauƙi da:
zogale
habbatus sauda
zuma da citta
(A kula: a yi shawarar likita idan matsala ta tsananta) - Ganin likita
Idan rikicewar al’ada ta daɗe, likita zai iya yin gwaji don gano matsalar hormone ko wata cuta.
Lokacin Da Ya Kamata Ki Je Asibiti
Idan haila ta tsaya fiye da watanni 3
Idan kina zubar jini mai yawa
Idan kina jin ciwo sosai
Idan kina neman haihuwa amma haila ta rikice - Da Karshe:
Rikicewar al’ada ba abu ne da ya kamata a raina ba. Da gyaran rayuwa, rage damuwa, da kulawar likita, yawancin mata suna samun sauƙi.






