Da yawa daga cikin ma’aurata hankalinsu ya tashi tun bayan da muka bada sanarwa akan wannan darasin na illar da yiwa mace sakace wato fingering yake da shi. Idan kana cikin mazan da hankalinsu ya tashi to kwantar da hankalinka ka natsu ka karanta wannan darasi domin ka fahimci abunda ake magana.
Mene ne Sakace?
Sakace, ko fingering a turance, wasa ne na motsa sha’awa da gaban mace ta hanyar saka mata yatsa a gabanta ana mata sakace har sai ta samu gamsuwa ko kuma an motsa mata sha’awar ta.
Masana sun tabbatar da cewa kusan sama da rabi na mata ta wannan hanyar suke samun gamsuwa cikin sauki maimakon shiga da fitan azzakari cikin farjin su. Don haka akwai matan da ko kwana aka yi akansu muddin ba wasa aka musu da gabansu da yatsa ko abunda yayi kama da hakan ba sam ba zasu taba samun gamsuwa ba.
Illolin da Sakace Yake Da Shi
Sai dai kuma wannan nau’in wasan da akasarin mata suke jin dadin sa, yana iya haifar musu da matsala muddin ba a kiyaye ba wajen aiwatar da wannan wasan ba. Da farko dai gaban mace waje ne da yake da matukar son kulawa da kiyaye wa. Don haka ba komai bane ake zuwa a cusa mata shi ba haka nan kawai da sunan motsa sha’awa ko gamsar da ita ba.
Cutar Ciwon Sanyi (Syphilis)
Cutar ciwon sanyi da ake kira Syphilis, cuta ce da za a iya cusawa mace a gabanta ta hanyar yi mata wasa da yatsa. Akwai mazan da basa kula da tsaftace faratansu, ko wanke hannu su domin tsaftace shi kamin kusantar matansu da wasa. Don haka muddin ba a tsafta ce farata da hannu ana iya sawa mace cuta a gabanta na ciwon sanyi.
Cutar HPV (Human Papillomavirus)
Akwai wata cutar da aka iya samunta ta shiga farce da ake kira Human papillomavirus (HPV). Wannan cutar tana shiga cikin farce ne ta boye, don haka da zaran a cusawa mace yatsa a gabanta mai dauke da kwayar wannan cutar zai jawo ta dauki wannan ciwon a gabanta.
Cutar Gonorrhea
Idan namiji yake ya tsokala yatsarsa gaban macen da take dauke da ciwon Gonorrhea amma bai sadu da ita ba, yazo ba tare da tsaftace hannunsa da faratansa ba ya dauki wannan yatsar ya cusa a gindin matarsa, to tana iya kamuwa da cutar na Gonorrhea cikin sauki.
Yadda Maza Suke Yada Cutuka Ga Matansu
Maza da damar gaske suke zuwa waje su kwaso irin wadannan cutukan su yadawa matansu daga bisani kuma suzo suna zargin matan nasu da zina. Domin shi kila yasan bai yi Jima’i da wata ba, amma dai ya mata wasa da yatsa, sai kuma ace matarsa ta kamu da cutar da ake kamuwa ta hanyar Jima’i da shi babu a tare da shi. Wannan zai sa a samu gardama da zargi, bayan shine ya kwaso cutar ta hanyar wasa da gaban






