Wannan tambaya ce da mutane da yawa suke jin kunyar yi, amma muhimmiyar tambaya ce ta addini. Wata ‘yar’uwa ta tambayi hukuncin tsotson azzakarin miji da kuma wasan farji da harshe kafin saduwa.
Amsar Malamai
Hakan ya halatta a sharian Musulunci. An rawaito halaccin haka daga magabata, ciki har da Imamu Malik (Allah ya yi masa rahama).
Sharuɗɗan da ake bukata:
- A tabbatar an tsaftace wurin sosai, musamman farjin mata
- Wasu likitoci suna ba da shawarar wanke wurin da gishiri kafin yin haka, domin kariya
Hujjar Sharia
Allah Madaukakin Sarki ya ce a Suratul Bakara, aya ta 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona. Wannan yana nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji daɗi da su – sai dai dubura, wadda nassi ya haramta.






