Saduwa tsakanin miji da mata wani bangare ne mai muhimmanci a rayuwar aure. Sai dai akwai wasu matsaloli da ke iya shafar lafiyar mace idan ba a kula da su ba.
Daya daga cikin wadannan matsaloli shi ne rashin kuka (lubrication) a lokacin saduwa.
A wannan labarin, za mu yi bayani kan illar da rashin kuka ke haifarwa ga mace, sanadin hakan, da kuma hanyoyin magancewa.
Menene Kuka (Lubrication)?
Kuka shi ne ruwan jiki da farji yake samarwa a lokacin da mace ta ji sha’awa. Wannan ruwa yana taimakawa wajen:
- Saukaka shigar azzakari
- Rage gogayya da zafi
- Kare bangon farji daga rauni
- Sa saduwa ta yi dadi ga bangarorin biyu
Illolin Rashin Kuka Ga Mace
1. Zafi da Rashin Jin Dadi
Idan babu isasshen kuka, saduwa za ta zama mai zafi ga mace. Wannan na iya sa ta ki sha’awar saduwa gaba daya.
2. Raunuka da Tsagewar Farji
Gogayya marar ruwa na iya haifar da kananan raunuka ko tsagewar fatar farji. Wannan na iya kawo:
- Zub da jini
- Kumburi
- Ciwo bayan saduwa
3. Kamuwa da Cututtuka
Raunukan da suka faru na iya zama hanyar shigar kwayoyin cuta, wanda ke kara hadarin kamuwa da:
- Cututtukan al’aura (STIs)
- Cutar mahaifa
- Infection daban-daban
4. Matsalar Haihuwa
Idan matsalar ta ci gaba, tana iya shafar mahaifa da kuma iya haifar da matsala wajen daukar ciki.
5. Damuwa da Tashin Hankali
Mace da ke fama da wannan matsala na iya shiga cikin damuwa, kunya, ko jin cewa ba ta cika wa mijinta bukata ba.
Sanadin Rashin Kuka
- Rashin isasshen lokacin sha’awa (foreplay) – Wannan shi ne babban sanadi
- Damuwa da tashin hankali
- Canjin hormones – musamman lokacin shayarwa, bayan haihuwa, ko menopause
- Wasu magunguna
- Rashin lafiya
- Rashin sha ruwa sosai
Hanyoyin Magancewa
Kara Lokacin Sha’awa (Foreplay)
Miji ya kamata ya ba mace isasshen lokaci kafin saduwa don jikin ta ya shirya.






