Mafi yawan mata da wasu samari suna tambayar cewa nonon budurwa ko sabuwar Amarya yana ruwa kuwa. wannan post zai baku amsar tambayar ku.
Abinda yakamata ku sani game da nonowan budurwa ko sabuwar Amarya, shine:
- 1. Budurwa ko sabuwar amarya da ba ta haihu ba:
Nononta ba zai fitar da ruwa ba a dabi’ance, domin:
- Ba ta haihu ba,
- Ba ta dauki ciki ba,
- Ba ta samu canjin hormone da ke sa nono ya fitar da nono ba.
2. Amma wani lokacin ana iya ganin dan ruwa ko danshi:
- Idan ana shafar nono sosai, wasu glands na fata a kan nono sukan fitar da ɗan danshi mai kama da man shafawa shi wannan ba ruwan nono ba ne.
- Wannan ba cuta ba ne kuma ba alama ce ta ciki ba.
3. Yaushe ne nonon mace ke fitar da ruwa da gaske?
- Cikin daukar ciki Hormone na prolactin na motsa samar da nono
- Bayan haihuwa Domin Shayar da jariri
- Matsala a hormone Wani lokaci galactorrhea nono yana fitar da ruwa ba tare da ciki ba
- Infection ko ciwo Idan nono yana zafi, kumburi, ko yana fitar da ruwa mai wari ko launi
Idan mace ta fitar da ruwa daga nono ba tare da ciki ba, ko ciwo a jiki, to ya kamata tanemi magani don tabbatar da ba wata matsala ba ce.
Allah ya kara lafiya da tsarewa, Aamin.






