A lokacin daukar ciki, musamman daga wata na biyu zuwa sama, ana bukatar a kula da irin kwanciyar da ake yi yayin jima’i domin:
Kariya ga mace
Kaucewa matsin lamba akan ciki
Tabbatar da lafiyar jariri
Ga wasu kwanciyoyi da ake ba da shawara:
- Side-by-side (kwance gefe)
Mijin yana kwance a bayansa, matar kuma a gabansa suna fuskantar juna ko baya:
Wannan hanya ce mai sauki, bata takura wa ciki ba.
Yana da kyau musamman daga wata na 4 zuwa 9.
- Matar a saman miji (woman-on-top)
Yana bada dama matar ta sarrafa zurfi da nauyi.
Ciki baya samun matsin lamba.
Amma idan ciki yayi girma sosai, zai iya wahala.
- Doguwar kwanciya (spooning style)
Mijin na baya, matar na gaba suna kwance.
Wannan kwanciyar na hana nauyi ya matsa kan ciki.
Yana da dadi da kariya.
- Matar a gefen gado (edge of bed)
Matar tana kwance gefen gado, mijin na tsaye ko durkushe.
Wannan hanya na hana matsin lamba akan ciki.
Hanyoyin da ya kamata a guje wa:
Matar a kasa, mijin a sama (missionary position) daga wata na 4 sama – zai iya matsa wa ciki.
Duk wata hanyar da ke takura wa mace ko ciki – ana guje wa.
Karin Shawara:
Idan akwai wata matsala ta lafiya (kamar ciwon mahaifa, zubar ciki da dai sauransu), ana shawarar a nemi likita kafin a ci gaba da saduwa.
Jima’i ba laifi bane a ciki muddin likita bai hana ba.
A kullum ana bukatar nutsuwa da fahimtar juna tsakanin ma’aurata.
Allah Ya ba da lafiya, ya sauke lafiya.
Kuyi Sharinga Domin Wasu Su Amfana!






