Da yawa daga cikin ma’aurata suna fara soyayya cikin annashuwa, cike da kulawa da kalmomin da ke sanyaya zuciya. Sai dai, bayan an yi aure, abubuwa sukan fara sauyawa:
IN DA MATSALAR TAKE
- RASHIN KULAWA DA JUNA BAYAN AURE: Abin da ake yi kafin aure – kira, saƙo, yabo, da nishadi – ana barinsa bayan an zama miji da mata.
- SHIGOWAR NAUYIN RAYUWA: Rayuwar aure tana da nauyi: cefani, tarbiyya, girki, aiki… Hakan yana shafar lokacin soyayya idan ba a yi hankali ba.
- RASHIN FAHIMTA DA YAWAN ZARGI: Idan matsaloli sun fara bayyana, ba a tattauna su cikin natsuwa. Zargi da zafi sukan karya zaman lafiyar zuciya.
- DAUKAR JUNA DA WASA: Wasu suna ganin yanzu tunda sun auri juna, babu buƙatar ƙoƙari. Sai soyayya ta fara dusashewa.
HANYAR MAGANCE HAKAN :
- A TUNA CEWA SOYAYYA BUƘATAR KULAWA TAKE: Kamar yadda ake shuka ƙauna da ruwa kafin aure, haka ake buƙatar yi bayan aure — da kalmomi masu daɗi, kyaututtuka, da kulawa.
- A ƘARFAFA SADARWA TSAKANIN MA’AURATA: Tattaunawa cikin salo da girmamawa yana taimakawa rage kuskure da tsinkaye tunanin juna.
- A DAWO DA ABUBUWAN DA SUKA FARA DA SU: Idan kuna tura saƙonni masu daɗi kafin aure, me yasa kuka daina yanzu? Soyayya tana daɗuwa da ƙanƙanin kulawa.
- A FAHIMCI JUNA, A KOYI YAFE JUNA: Rashin yafe wa yana gina gabar da ke kashe ƙauna. Ki yi haƙuri, ka yi haƙuri — ku zama garkuwar juna.
- A HAƊA ADDU’A DA ƘOƘARI: Soyayya ta gaskiya bata dorewa sai da taimakon Allah. A nemi zaman lafiya da albarka a cikin aure.
A karshe, Soyayya tana ƙara da ƙoƙari, tana raguwa da sakaci.






