ArewaJazeera
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home
Saturday, January 17, 2026
  • Login
No Result
View All Result
No Result
View All Result
ArewaJazeera
No Result
View All Result
Home Zamantakewa

Shawara Ga Amarya Ko Wacce Ta Kusa Aure

Malamar Aji by Malamar Aji
January 1, 2026
in Zamantakewa
0
Shawara Ga Amarya Ko Wacce Ta Kusa Aure

Shawara na musamman ga sabbin amare ko wanda ta kusa aure.

  1. Tun daga farko amarya tsarkake zuciya ya kamata kiyi kisa a zuciyar ki cewa aure zakiyi kuma bautar Ubangiji zaki je, musamman idan mai mata zaki aura ki nufe ta da zuciya mai kyau.

  2. Ki saka a zuciyar ki don Allah zaku zauna da wanda kika samu, idan ke kadai ce ma duk daya ne.

  1. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kadai kamar ana sauran sati daya bikin naki.

  1. Haka ma magungunan Musulunci da ka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu.
  2. Wadannan za su warkar miki da duk wani rauni ko cikas da kila kina da shi a lafiyar jikinki da ta ruhinki gaba daya.

  1. Sai kuma ki rika yawan shan ruwa, a kalla ki sha kofi takwas na ruwa kullum.

  1. Amarya babu ruwan ki dayin wani bleaching saboda b’ata kalan fatarki zakiyi,da yawa amare idan za’a yi auran su wasu bleaching sukeyi wai don suyi haske, sai nake ganin mijin yafi ki sani kalan ki yadda kike (ina maganar da bakar mace ce mai canja halittan Allah) ba’a hanaki gyara ba amma kiyi gyara mai kyau ga mayukan gyaran jiki masu kyau wanda zai gyara miki jikin ki,irin su zaki samu masu kyau kiyi gyaran da duk wanda ya ganki yasan bawai bleaching bane saboda yanzu akwai kalan ‘yan gayu akwai kuma kalan bleaching don haka Amarya sai kiyi kalan gayu.

  1. Amarya idan kinje kin samu mai mata don Allah ki zauna da ita lafiya kuma ki rike ‘ya’yan mijin ki idan kika jawo su jikin ki babu yaron da zai miki rashin kunya saboda zuciya tana son mai kyautata mata.

Kwalliya da ado da zuba kamshi naki ne domin macen datasan kanta kullum cikin kamshi take a ko ina.

  1. Amarya a yayin shagalin bikin ki don Allah karkiyi abinda zaki zubar da albarkan auran ki karkiyi irin rashin kunyar da wasu amaren zamanin nan sukeyi,ko kuma irin shigar fitsara wanda bai dace ba.

  1. Amarya ki sani cewa dukkan wata soyayyar da kukayi kafin aure ba soyayyah bace, yanzu ne soyayyah yanzu ne idan zama ya hadaku da juna kowa zai San wanene a tsakanin ku, Yanzu ne zaku fahimci junanku.

Amarya karki yarda da zugan wasu kawayen domin akwai wasu kawayen da idan har zaki kasance mai daukar zugan su tsab zasu iya kashe miki aure, shiyasa ake son mutum tun farko ma yasan wane irin kawaye ya dace yana mu’amala dasu.

  1. Amarya karki shiga gidan mijin ki da wata munguwar niyya misali:
  2. yana da matarsa sai ki shiga da niyyar ai sai na fitar da ita.kinga tundaga waje tun farkon auran ki kin saka munguwar niyya a zuciyar ki ki gyara karki saka wannan tunanin a zuciyar ki.

  1. Amarya ki zama mai kawaici da kauda kanki a komai ma ba kowane abu bane sai kinyi magana wani abin hakuri ake yi.
  2. Sannan ki tsabtace zuciyarki da kyawawan shau’uka da tunani da kyautata zato da fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya tare da sauran dukkan ma’aurata Musulmi, Amin.

Danna Nan Don Samun Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Tags: #shawaraaAmarya #gidanmiji #zamanaure #uwargida

Related Posts

Amfanin Nishi Lokacin Saduwa – Me Yasa Ya Kamata Mata Su Yi?
Zamantakewa

Gaskiyar Game Da “Jikewa” A Farjin Mace — Me Hakan Yake Nufi?

January 16, 2026
Dalilin Da Yasa Wasu Mata Ke So A Dade Ana Wasa Kafin A Fara Jima’i
Zamantakewa

Dalilin Da Yasa Wasu Mata Ke So A Dade Ana Wasa Kafin A Fara Jima’i

January 16, 2026
Me Yasa Saurayi Ke Samun Natsuwa Idan Yana Soyayya Da Bazawara?
Zamantakewa

Me Yasa Wasu Mata Ke Son A Taɓa Su A Wasu Wurare Kafin A Kusanto Gabansu?

January 16, 2026
Abubuwan Da Ke Ƙara Ƙarfin Azzakari Ta Hanyar Lafiya
Zamantakewa

Abubuwan Da Ke Ƙara Ƙarfin Azzakari Ta Hanyar Lafiya

January 16, 2026
Lokuta 6 Da Mata Ke Fi Jin Sha’awar Kusanci Amma Kunya Ke Hana Su Faɗa
Zamantakewa

Lokuta 6 Da Mata Ke Fi Jin Sha’awar Kusanci Amma Kunya Ke Hana Su Faɗa

January 16, 2026
Sirrin Sautin Murya – Me Ya Sa Maza Ke So?
Zamantakewa

Karan Mace Lokacin Saduwa: Alamomin Gamsuwa Da Kuma Dalilan Rashin Faruwarsa

January 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

No Result
View All Result
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In