Rashin tashi ko Erectile Dysfunction (ED) matsala ce da ke shafar maza da dama a duniya, wannan post zai yi bayanin abunda ke kawo matsalar da hanyar daza a bi don magance matsalar.
Wannan matsala na nufin rashin iya samun ko riƙe tashi na azzakari lokacin saduwa, wanda zai iya kawo matsaloli a dangantakar aure da jin dadin ma’aurata.
Dalilan Rashin Tashi:
- Matsalolin Lafiya: Cututtuka kamar su ciwon zuciya, suga, da hawan jini na iya kawo ED.
- Damuwa da Tashin Hankali: Matsalolin zuciya da damuwa na rage sha’awa da kuma iya tashi.
- Rayuwar Zamani: Shan taba, shan giya, da rashin motsa jiki na iya kawo wannan matsala.
- Matsalolin Hormone: Rashin daidaiton hormone na iya shafar tashi.
- Amfani da Magunguna: Wasu magunguna na da illa ga tashi da sha’awa.
Hanyoyin Magance Matsalar:
- Neman shawara daga likita don gano asalin matsalar.
- Canza salon rayuwa zuwa mai lafiya da motsa jiki.
- Gujewa shan taba da giya.
- Amfani da magungunan da likita ya bada.
- Tattaunawa da abokin zama don rage damuwa da karfafa zumunci.
Da wannan hanyoyi, namiji zai iya samun sauki daga matsalar rashin tashi da kuma inganta rayuwar aure.
Ka raba wannan labarin domin maza su samu fahimta da taimako.






