Akwai manyan abubuwan da suke sa maza su runga jin azzakarin su na zafi bayan saduwa.
Ga abuwabuwan dake haddasa zafin azzakari:
1. Goge-goge mai tsanani
Idan farjin mace ya bushe ko ba a sami isasshen ruwan sha’awa ba, gogayyar fata da fata na iya haifar da jin zafi ko ƙuna.
Haka kuma saduwa da karfi ko ba tare da shiri ba na iya haddasa irin wannan zafin.
2. Tsananen jin motsi bayan releasing
Bayan releasing, azzakari yakan zama mai matuƙar sensitivity.
Idan aka ci gaba da saduwa ko aka taɓa shi da sauri, zaka iya jin zafi ko kuna. Wannan ba matsala ce ta lafiya ba — halittar jiki ce kawai.
3. Ƙananan rauni
Wani lokaci ƙaramin fasa ko karce na iya faruwa yayin jima’i, musamman idan babu isashen ruwa daga mace ko an yi jima’i da karfi.
4. Ciwon bututun fitsari
Domin maniyyi na fitowa ta bututun fitsari, idan akwai ƙaiƙayi, kumburi ko kamuwa da wani irin infection, zaka iya jin zafi yayin releasing ko bayan haka.
5. Rashin jituwa da condoms, gel ko sabulu
Wasu na samun matsalar fata daga latex, lubricants ko sinadarai da ke cikin condoms ko gel, wanda ka iya janyo zafi ko kaikayi.
6. Infections
Wasu cututtuka kamar urethritis, chlamydia ko gonorrhea na iya haifar da zafi, fitsari mai ƙuna, yawan fitsari, ko fitar ruwa mai wari daga azzakari.
Me zaka kula da shi a jikinka?Idan zafin yana faruwa ne bayan round na farko kuma baya maimaituwa, yawanci ba matsala ce mai tsanani ba. Yana iya zama sensitivity ne ko goge-goge kawai.
Amma ka tuntuɓi likita idan:Zafi baya daina har bayan saduwa,Zafin yana maimaituwa,Kana jin zafi lokacin fitsari,Kana fitar wani ruwa mai wari ko launi.
Abubuwan da zaka iya yi idan ba ka da alamun infectionKa tabbatar mace tana da isasshen ruwa na sha’awa kafin ku fara.Idan ba ku da shi, amfani da lubricant mai kyau zai taimaka.
Kada ka cigaba da jima’i nan da nan bayan releasing na farko; bari jiki ya dan huce.
Ka guji sabulun da ke busar da fata ko haifar da kaikayi.Ka sha ruwa sosai, sannan ka rika cin abinci mai kyau tare da multivitamin da zinc domin lafiyar azzakari.
Idan matsalar ta maimaitu ko ta tsanantaKa je wajen likitan urology ko a STD Clinic domin a duba ka, a yi gwaji, a kuma ba ka magani idan an sami infection.






