Akwai lokuta na musamman da mace ta fi samun ciki. Sanin waɗannan lokuta zai taimaka wa masu neman ciki da masu neman tazara.
Akwai lokuta na musamman a jikin mace da suka fi dacewa da ɗaukar ciki. Ana kiran su lokutan haihuwa (fertile period). Sanin su yana da amfani.
Menene Ovulation?
Ovulation shine lokacin da ƙwai ke fitowa daga mahaifa. Yana faruwa sau ɗaya a kowane wata. Yawanci rana ta 14 idan zangon haila kwanaki 28 ne.
Yadda Ake Lissafa Lokutan Haihuwa
- Ƙidaya daga rana ta farko da haila ta fara
- Cire kwanaki 14 daga jimillar kwanakin zangon haila
- Kwanaki 5 kafin ovulation da rana 1 bayan ta – su ne lokutan da ciki yake shiga
Misali:
- Zangon haila = kwanaki 28
- Ovulation = rana ta 14
- Lokutan ciki = rana ta 10 zuwa ta 15
Ga Masu Neman Ciki
- Ku yi jima’i kullum ko kowace rana 2 a lokacin fertile
- Ku yi kafin da bayan ranar ovulation
- Ku kasance cikin natsuwa
Ga Masu Neman Tazara
- Ku guji jima’i a kwanakin fertile
- Ku yi jima’i a kwanakin da ba fertile ba
- Wannan yana buƙatar kulawa da jikin mace
Alamomin Ovulation
- Zafi kaɗan a ƙasan ciki
- Ruwa mai kauri daga farji
- Ƙaruwar sha’awa
- Ƙaruwar zafin jiki da safe
Sanin lokacin da ciki yake shiga:
- Yana taimaka wa masu neman haihuwa
- Yana taimaka wa masu neman tazara
- Ilimi ne da kowane ma’aurata suke buƙata
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Aure Da Soyayya
Ayi share sannan ayi comment don wasu su amfana






